
Ministan tsaro, Muhammad Badaru ya Ajiya mukaminsa inda ya bayar da dalilin rashin lafiya.
Badaru ya aikewa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da wasikar ajiye aikin a ranar 1 ga watan Disamba.
Kuma me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce shugaba Tinubu tuni ya amince da wannan ajiye aikin inda ya godewa Badaru bisa gudummawar da ya bayar.