
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya karawa shugaban Kwastam, Bashir Adeniyi yawan wa’adinsa.
Me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
Sanarwar tace shugaban kwastam din, Mr. Bashir Adewale Adeniyi, MFR ya kamata ya ajiye aiki nan da 31 ga watan Augusta 2025.
Amma an kara masa wa’adi zuwa shekara daya.
Sanarwar tace an kara masa wa’adinne dan ya ci gaba da ayyukan gyara Najeriya sannan shugaba Tinubu ya yaba da aikinsa.