
Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban sojojin Najeriya, General OO Oluyede ya koma jihar Borno da zama dan kula da yanda sojoji ke aikin magance matsalar tsaro.
A ‘yan Kwanakinnan dai Hare-haren kungiyar Bòkò Hàràm sun yawaita inda aka gansu da makamai na zamani.
Majalisar tarayya ma ta bayyana cewa, ‘Yan Bòkò Hàràm din sun fi sojojin Najeriya makamai masu kyau.
Wasu na ganin komawar shugaban sojojin zuwa jihar Borno zai taimaka matuka wajan magance matsalar tsaron jihar da makwabciyarta Yobe.