Friday, December 5
Shadow

Da Duminsa: Sojoji 2 cikin wadanda akw zargi da yunkurin yiwa shugaba Tinubu Jhuyin mulki sun tsere an nemesu an rasa

Rahotanni sun ce 2 daga cikin sojojin da ake zargi da yunkurin yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Jhuyin mulki sun tsere.

Jaridar Cable ce ta ruwaito labarin inda tace cikinsu akwai JM Ganaks wanda ke da mukamin Major da lambar aiki N/14363 sannan yana aiki ne a Jaji.

Sannan akwai G Binuga wanda shi kuma Captai ne me lambar aiki N/167722 wanda dan Asalin jihar Taraba ne.

Thecable tace zuwa yanzu akwai sojoji 30 da ake tsare dasu ake tuhumarsu bisa zargin yunkurin yin Jhuyin mulkin.

Karanta Wannan  Sheikh Ɗahiru Bauchi dattijo ne mai son zaman lafiya - Kwankwanso

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *