Monday, October 12
Shadow

Da Duminsa: Wani babban dan siyasa ya fallasa yanda Kwankwaso kewa Shugaba Tinubu aiki a boye

A yayin da Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya fito ya bayyana tabbacin hadewarsa da Peter Obi inda yace zai masa mataimakin shugaban kasa a takarar 2027.

Rahotanni daga Marali Radio TV sun bayyana cewa, Tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya tonawa Kwankwaso Asiri kan yanda yakewa Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu aiki a boye.

A cewar kafar, Malam Ibrahim Shekarau yace gara su a bayyane sukewa Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu aiki, amma shi Kwankwaso ai a boye yakewa shugaban aiki.

Zuwa yanzu dai Kwankwaso bai ce uffan kan wannan zargi ba.

Karanta Wannan  Gawuna yaki daga waya yayin da shugaba Tinubu ke ta kokarin kiransa dan hanashi komawa Kwankwasiyya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *