Tuesday, March 10
Shadow

Da Duminsa: ‘Yan Bìnďìgà sun sake kaiwa wutar lantarkin Najeriya hari

Rahotanni daga jihar Kogi sun bayyana cewa, ‘yan Bindiga sun sake kaiwa tashar wutar lantarki da hukumar TCN ke kan ginawa hari.

Tashar wutar lantarkin tana garin Obajanane.

Me kula da yada labarai na kamfanin, Ndidi Mbah ne ya tabbatar da hakan inda yace an kai harinne da daren ranar Talata.

Jami’an tsaron dake gadin tashar wutar sunce maharan na zuwa suka bude wuta suna harbin kan mai uwa da wabi wanda hakan yasa suka tsere.

TCN tace a yanzu tana bincike dan ganin irin girman barnar da maharan suka yi.

Karanta Wannan  Hutun Sallah da jihar Kano ta baiwa Makarantu yayi yawa, Inji 'yan Kudancin Najeriya yayin da suke caccakar gwamnatin jihar suna cewa dama 'yan Arewa basu san muhimmancin ilimi ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *