Tuesday, March 17
Shadow

Da Duminsa: Za’a mayar da Malam Nasiru Ahmad El-Rufai gidan gyara hali na Kaduna bisa sabbin zarge-zargen da ake masa

Rahotanni sun bayyana cewa hukumomi na shirin mayar da malam Nasiru Ahmad El-Rufai jihar Kaduna dan ci gaba da tsareshi a can.

Hakan na zuwane yayin da ake shirin fara shari’ar sa akan wasu sabbin zarge-zargen da ake masa.

Hakan ya fito ne daga Sahara Reporters inda tace ta samu rahoton daga majiya me karfi.

Saidai bata bayyana sabbin zarge-zargen da akewa El-Rufai ba.

Majalisar jihar ta Kaduna dai ta bayyana yin bincike da gano aikata ba daidai ba a zamanin Malam Nasiru Ahmad El-Rufai na Gwamnan Kaduna.

A yanzu dai malam Nasiru Ahmad El-Rufai na tsarene a hannun Hukumar ICPC.

Karanta Wannan  'Yan majalisar Wakilai 2 sun bar jam'iyyar PDP da Labour Party zuwa APC

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *