Sunday, March 29
Shadow

Da Duminsa:Hukumar zabe me zaman kanta INEC ta sanar da ranar da za’a yi zaben shugaban kasa na shekarar 2027

Hukumar zabe me zaman kanta INEC ta sanar da ranar 20 ga watan Fabrairu na shekarar 2027 a matsayin ranar da za’a gudanar da zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Shugaban Hukumar zaben, Professor Joash Amupitan ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja ranar Juma’a.

Yace zaben shugaban kasa dana ‘yan majalisun tarayya za’a yishi ne ranar 20 ga watan Fabrairu inda kuma zaben Gwamnoni dana ‘yan majalisar jihohi za’a yishi ne ranar 6 ga watan Maris.

Ya bayyana cewa, sun shirya tsaf dan gudanar da zaben.

Karanta Wannan  Bamu yadda ba, A mayar dasu gida, wane irin aiki ne zasu yi wanda matasanmu ba zasu iya yi ba? NLC ta jihar Legas ta yi gargadi kan matasa 89 daga Arewa da aka kai Su yi aiki a matatar man Dangote dake Legas

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *