
Babbar Kotun tarayya dake Abuja ta kwace kujerar dan majalisar wakilai, Abubakar Gummi bayan da ya bar jam’iyyar PDP zuwa APC
Abubakar Gummina wakiltar mazabun Gummi/Bukkuyum ne a majalisar wakilai ta tarayya.
Mai shari’a, Obiora Egwuatu ne ya yanke wannan hukunci inda yace kada kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas ya sake kallon Abubakar Gummi a matsayin dan majalisar.
Hakanan alkalin ya kuma baiwa hukumar zabe me zaman kanta INEC umarnin sake shirya wani zabe dan cike gurbin dan majalisar nan da kwanaki 30.