Friday, December 5
Shadow

Da Duminsu: Shugaban kasar Amurka Donald Trump zai haramtawa ‘yan Najeriya shiga Amurka

Shugaban kasar Amurka Donald Trump na shirin dakatar da karin kasashe 36 daga shiga kasar Amurkar kuma ana tsammanin Najeriya ka iya shiga ciki.

A cikin kasashen da Trump din ke shirin dakatarwa akwai kasashen Afrika guda 25 ciki hadda kasar Egypt da Djibouti sannan akwai kasashen Asia.

Kafar the Washington post ta kasar Amurkar tace ta yi kokarin jin ta bakin fadar White House amma abu ya ci tura.

Karanta Wannan  Na baiwa Jami'an tsaro umarni da kakkausar murya su gaggauta kawo karshen matsalar tsàròn Najeriya>>Shugaba Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *