
Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa gara wani daga kudu ya sake zama shugaban kasa da Tinubu ya sake zama shugaban kasa a shekarar 2027.
El-Rufai ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV.
Yace bai da tabbacin nan da lokacin zaben 2027 ko zai ci gaba da dama a Jam’iyyar APC.
El-Rufai ya zargi Tinubu da nada yaransa mafi yawanci yarbawa a mukaman siyasa.