
Da yiyuwar Tinubu ba zai iya tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027 ba idan Amurka ta saki bayanai kan safarar miyagun kwayoyi da tace yayi.
Ana zargin dai Shugaban kasa Tinubu da wasu mutane 3 a shekarun 90s sun yi safarar kwayoyi a birnin Chicago na Jihar Illinois ta kasar Amurka.
An yi shari’a dan yanke musu hukunci amma ba’a san inda aka kwana ba
Lauyoyi da ma sauran masu fafutuka na ta neman hukumar FBI da DEA su saki bayanai kan lamarin amma sai jan kafa suke inda lamarin ya dauki shekaru.
Wasu dai na zargin akwai wata kullalliya a kasa game da kin fitar da bayanan.