
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya soki dakatar da gwamnan jihar Rivers da mataimakiyarsa da ƴanmajalisar dokokin jihar, wanda shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya yi.
Jonathan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a matsayin shugaban taro wanda gidauniyar Haske Satumari ta shirya a ranar Asabar a Abuja, inda ya bayyana rashin jin daɗinsa kan matakin na cire zaɓaɓɓun shugabanni.
“Wannan matakin da aka ɗauki zai ɓata sunan Najeriya ne a idon duniya,” in ji shi, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.
Jonathan ya ce duk da cewar akwai buƙatar ɗaukar matakan da za su magance rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar Rivers na tsawon lokaci, a cewarsa dakatar da waɗanda mutane suka zaɓa a matsayin shugabanninsu bai dace ba.
Ya ƙara da cewa ya san bai kamata a matsayinsa tsohon shugaban ƙasa ya cika maganganu barkatai a game da abubuwan da suke a ƙasar ba, amma “yadda ake kallon Najeriya yana ta’allaƙa ne a kan matakan ɓangaren zartaswa da majalisa da na shari’a suka ɗauka,” in ji shi.