Thursday, February 26
Shadow

Dala Biliyan $3.6 ‘yan Najeriya suka rika kashewa duk shekara wajan zuwa kasashen waje neman magani a zamanin Buhari

.Rahotanni sun ce a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ‘yan Najeriya sun kashe jimullar dala Biliyan $29.29 wajan zuwa kasashen waje neman magani.

Hakan na nufin ‘yan Najeriya sun rika kashe akalla dala $3.6 duk shekara wajan neman magani a kasashen waje a shekaru 8 da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi yana mulki.

Hakan ya bayyana ne daga bayanan da babban bankin Najeriya, CBN ya fitar.

Hakan ya nuna irin yanda ‘yan Najeriya suka dogara da kasashen waje wajan neman magani.

Karanta Wannan  Muna nan akan Bakanmu, kowa sai ya biya Haraji, ko ta hanyar halarar ya samu kuri ko bata ta hanyar halal ba, Qaruwai, Kwandastan Mota, dama kowace irin sana'a kake nan da 2026 sai ka fara biyan Haraji>>Inji Gwamnatin Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *