
Dan majalisar Tarayya wanda shine shugaban kwamitin dake kula da babban birnin tarayya, Abuja, Mukhtar Aliyu Betara ya bayyana cewa, tabbas an raba musu dala $5000 da ake ta rade-radi.
Saidai yace ba kamar yanda ake yadawa ba wai cin hanci ne aka basu dan su amince da tsige gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara bane.
Yace an basu kudin e a matsayin barka da sallah wanda kuma dama an saba duk shekarar ana basu.
Dan jarida, Jafar-Jafar ne ya bayyana haka inda yace yayi magana da dan majalisar.