Monday, March 16
Shadow

Daliba ‘Yar Shekara 15 Ta Zama Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina Na Wucin-Gadi Na Tsawon Mintuna Biyar

Daliba ‘Yar Shekara 15 Ta Zama Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina Na Wucin-Gadi Na Tsawon Mintuna Biyar

Daga Comr Nura Siniya

Shugaban majalisar dokokin jihar Katsina Hon. Nasiru Yahaya Daura, ya miƙa ragamar shugabancin majalisa na minti 5 ga wata ɗaliba mai hazaƙa Marwa Nasir Yahaya, a lokacin da daliban makarantar suka kawo ziyarar duba ayyukan majalisar, domin sanin makamar aiki, a ranar Litinin 19 ga watan Mayu 2025.

Katsina Reporters ta samu cewa, daliban makarantar “Little Angel ne suka zaɓi Marwa Nasir Yahaya, saboda kwazonta ga harkar ilimin addini da na zamani.

Ɗalibar dai ta kasance ɗiya ga shugaban majalisar dokokin na jihar Katsina.

Karanta Wannan  Bawai son Tinubu ne yasa 'yan siyasa ke tururuwar shiga APC ba, Kudin da suka sata na al'umma ne suke neman a yafe musu>>Solomon Dalung

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *