An samu dalibai biyu na jami’ar Federal Polytechnic Bida, dake jihar Naija wanda masoya ne sun mutu a daki daya.
Dalibar me suna A’isha ta mutu ne a dakin saurayinta me suna Akin wanda shima an iskeshi ya mutu.
Kafar Sahara Reporters data ruwaito labarin tace an samesu duka bakunansu da kumfa wanda ake kyautata zaton guba ce suka sha suka mutu.
Saidai zuwa yanzu babu wani karin bayani kan lamarin amma ‘yansanda sun dauki gawarwakin zuwa mutuware.
Hukumar makarantar tasu ma taki tace uffan kan lamarin.