
Bukatar rigar mama ta ganjo a wajen matan Legas na Karuwa, inda hakan ya kasance abin dubawa a jihar, kamar yadda jaridar Vanguard ta rawaito.
Wasu mata da jaridar ta zanta da su sun nuna cewa zaɓinsu na rigar mama ya dogara ne kan dalilai kamar araha da kuma ƙarko.
Da yawan matan Legas na sayen rigar mama ta gwanjo, wacce aka fi sani da “Okrika” saboda suna samuwa da yawa, ga araha, kuma su na da kyau.
Vanguard ta gano cewa baya ga manyan kasuwanni kamar Tejuosho, Balogun, da Katangowa a Legas, ana iya samun rigar mama na Okrika a ƙananan kasuwanni, shaguna, da wuraren masu sayar da kaya a gefen hanya.
Mrs Peace Okeke, wadda ake kira “Lady Bra” a tsakanin kwastomominta a Festac Town, yankin Amuwo Odofin, ta ce ta kwashe fiye da shekaru 18 ta na wannan sana’a.
A cewarta, tun da ta fara wannan sana’a, yawancin kwastomominta sun amince da ingancin rigar mama ta Okrika.
Okeke, wadda ke sayar da duka sabbi da kuma tsofaffin, ta ce waɗanda ke neman araha da ƙarko sun fi sayen na gwanjo.