Monday, March 24
Shadow

Dalilin da ya sa Gwamnatin Tarayya ba ta fara biyan kananan hukumomi kudadensu kai tsaye ba – ALGON

Gwamnatin Tarayya ba ta fara bayar da kudaden kasafi kai tsaye ga Kananan Hukumomi ba saboda ana ci gaba da bin wasu hanyoyin aiki, in ji Kungiyar Kananan Hukumomin Najeriya (ALGON).

Shugaban kwamitin amintattu na ALGON, Odunayo Alegbere, ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Abuja bayan wani taron kungiyar. Ya bayyana cewa an umarci kananan hukumomi da su bude asusu a Babban Bankin Najeriya (CBN) domin saukaka aiwatar da tsarin rabon kudade kai tsaye.

Duk da cewa har yanzu ba a kammala tsarin ba, Alegbere ya jinjinawa Gwamnatin Tarayya kan ci gaban da aka samu, yana mai cewa hukuncin da Kotun Koli ta yanke kan ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi babbar nasara ce. Ya jaddada cewa gwamnati na aiki don aiwatar da wannan hukunci, wanda ya hada da ‘yancin gudanarwa da kuma ‘yancin siyasa ga kananan hukumomi.

Karanta Wannan  Gwamnatin Sokoto ta ƙaddamar da tallafin azumi ga masu buƙata ta musamman

Ya tabbatar da cewa rabon kudade kai tsaye zai taimaka wajen yaki da talauci a matakin tushe, domin hakan zai bai wa kananan hukumomi damar mallakar cikakken iko a kan kudaden su da kuma aiwatar da ayyukan ci gaba.

Daily Trust

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *