
Sanata Shehu Sani ya bayyana dalilin da yasa ya koma Jam’iyyar APC.
Sanata Sani ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na ChannelsTV.
Yace Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ne ya jawoshi ya koma Jam’iyyar ta APC. Yace dama can yana daga cikin wadanda suka kafa jami’iyyar a Kaduna har aka ci zabe.
Yace sun samu rashin jituwa da Gwamna El-Rufai ne a wancan lokacin shiyasa suka bar Jam’iyyar kuma yanzu Gwamna Uba sani ya dawo dasu.