
DA DUMI-DUMI: Miji Ya Kashe Matarsa a Bauchi Saboda Abincin Buda Baki.
Rundunar ‘Yan Sanda Ta Fara Bincike Kan Kisan Wasila Abdullahi
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta fara bincike kan wani mummunan lamari da ya faru a daren Asabar, 1 ga Maris, 2025, inda wani attajiri mai suna Alhaji Nuru Isah, mai shekaru 50, ya buge matarsa, Wasila Abdullahi, mai shekaru 24, har lahira.
Bayanan da aka tattara sun nuna cewa rikici ya barke tsakanin ma’auratan ne a gidansu da ke kusa da makarantar GG Bauchi a unguwar Fadamam Mada, kan yadda za a raba kayan abinci da ‘ya’yan itatuwa don buda baki a watan Ramadan. Wani makwabci ya ce takaddamar ta rikide zuwa fada, inda Alhaji Nuru Isah ya dauki sanda ya bugi matarsa, wanda hakan ya sa ta fadi sumammiya.
Bayan haka, an garzaya da ita asibitin koyarwa na ATBU domin ceton rayuwarta, amma likitoci suka tabbatar da mutuwarta.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Wakili, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa wanda ake zargi yana hannun ‘yan sanda, kuma bincike na ci gaba.
Lamarin ya tayar da hankalin al’ummar yankin, inda jama’a ke kira ga hukumomi da su tabbatar da adalci ga marigayiyar.
Allah ya jikanta da rahama!
Inside Bauchi State