
Jam’iyyar PDP ta sanar da cewa, dan kudu zata tsayar takarar shugaban kasa a shekarar 2027.
Jam’iyyar ta bayyana hakane a zaman masu ruwa da tsaki da ya wakana a jiya.
Sannan ta canja wajan da zata gudanar da taronta na zaben shuwagabannin jam’iyyar wanda a da za’a yi a Kano, yanzu a jihar Oyo za’a yi.
Ana zargin an yi hakanne dan shiryawa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinda hanya a shirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2027.
Saidai hakan kuma zai zama koma baya ga Nyesom Wike wanda tuni dangantaka tsakaninsa da Gwamna Makinde ta yi tsami.