
Dan Najeriya, Sunusi Danjuma Ali da aka turawa Dala dubu 135 a wallet dinsa na Crypto watau kwatankwacin Naira Miliyan 200 bisa kuskure ya mayarwa da me kudin kudinsa.
An tura masa kudinne a Wallet dinsa ta Bitunix inda yana ganin hakan ya tuntubi wakilan kamfanin kuma suka tabbatar kuskurene aka yi wajan tura masa kudin.

Nan da nan aka warware.