Thursday, February 26
Shadow

Dangote na sayarwa da kasashen waje mai a farashi me sauki fiye da Najeriya>>’Yan kasuwar mai suka koka

‘Yan kasuwar man fetur sun koka da cewa, Dangote na sayarwa da kasashen waje man fetur a farashi me sauki fiye ye da yanda yake sayarwa a Najeriya.

”Yan kasuwar sun ce ‘yan kasar waje na samun ragin kusan Naira 65 akan kowace Lita idan aka kwatanta da farashin man da Dangoten ke sayarwa a Najeriya.

Dan hakane ma suka ce wani lokacin basa saye a wajan Dangote sai su je wajan ‘yan kasar wajen da ya sayarwa su saya a hannunsu su shigo dashi Najeriya.

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar DAPPMAN, Olufemi Adewole ne ya bayyana haka ga manema labarai na Punchng.

Yace abinda suke nema a wajan Dangote shine ya rika musu sauki dan haka sai su daina shigo da man daga kasashen waje suna saye a hannunshi.

Karanta Wannan  Sanata Lado ya miƙa kyaututtukan gidaje ga waɗanda su ka yi na ɗaya da na biyu a musabaƙar Kur'ani a Kano

Yace Dangote da gangan yake karya farashin mai da zarar ya ga sun kawo mai daga gasashen waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *