Kamfanin Dangote ya bayyana cewa manyan kamfanonin dakw hakar man fetur a Najeriya na kasa da kasa da ake kira da IOCs na yin dukkan mai yiyuwa dan ganin matatar mansa ta durkushe.
Mataimakin shugaban kamfanin na Dangote reshen matatar man, Devakumar Edwin ne ya bayyana haka.
Yace kamfanonin na sa farashi fiye da yanda yake a kasuwa ga Dangote wanda hakan ya sa shi kuma dole yake zuwa kasashen Amurka dan sayo danyen man da zai tace.
Hakanan ya koka da hukumar NMDPRA wadda yace tana baiwa ‘yan kasuwa lasisi ba tare da bun ka’ida ba su kuma suna siyo gurbataccen man fetur da aka tace daga kasashen waje zuwa Najeriya.
Yace a cikin lasisin gina matatun man fetur 25 da gwamnati ta bayar a Najeriya, su kadai ne suka cika alkawarin kammalawa akan lokaci inda yace ko dan haka ya kamata gwamnati ta basu goyob baya wajan gudanar da ayyukansu yanda ya kamata da kuma samarwa da ‘yan Najeriya ayyukan yi.