Sunday, March 29
Shadow

Dole kowa ya gayawa Gwamnati yawan kudaden da yake samu kuma ya biya haraji nan da 31 Maris

Tarar Naira dubu Dari(100,000) ce duk wanda bai gayawa Gwamnati yawan kudin da yake samu ba sannan ya biya haraji nan da ranar 31 ga watan Maris zai biya.

Dokar tace kamin nan da ranar 31 ga watan Maris dolene kowane dan Najeriya ya gayawa Gwamnati yawan kudaden da yake samu sannan ya biya Haraji.

Hakanan dokar tace duk wanda bai yi hakan ba za’a ci shi tarar Naira dubu dari(100,000) sannan za’a ci gaba da cinsa tarar Naira dubu hamsin(50,000) kowane wata da yaki fadawa Gwamnati yawan kudaden da yake samu kuma yaki biyan Haraji

Yanda mutum zai gayawa Gwamnati yawan kudaden da yake samu shine:

Karanta Wannan  Da Duminsa: Tsohon Hadimin Shugaban kasa, Bashir Ahmad yayi karin haske game da rashin lafiyar shugaba Buhari

Ka samu Lambar biyan Haraji da ake cewa TIN.

Ka Shiga E tax portal na jiharka.

Saika cie duka bayanan da ake da bukata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *