Thursday, May 7
Shadow

Dolene Godswill Akpabio ya sauka ko mu tsigeshi>>Inji Sanata Adams Oshiomhole

Sanata Adams Oshiomhole ya caccaki kakakin majalisar Dattijai Godswill Akpabio saboda canja dokokin zama kakakin majalisar.

Adams Oshiomhole yace sabuwar dokar dake cewa sai mutum yayi shekaru 8 a matsayin sanata a jere kamin ya nemi shugabancin majalisar bata yi ba.

Yace idan kuwa aka ce za’a yi amfani da wannan doka to shi kamshi Sanata Godswill Akpabio dole ya sauka daga mukaminsa dan bai cika sharudan ba.

Yace kakakin majalisa da suka gabata irin su David Mark da sauransu sun yi shugabancin majalisar da dokokin da ake dasu ba tare da matsala ba.

Yace to a wane dalili za’a canja dokokin?

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda Kwankwaso da Peter Obi suka isa wajan babban taron jam'iyyar ADC a Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *