Sunday, April 12
Shadow

DSS na binciken hadiman Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf guda 5 saboda zargin batawa Kwankwaso suna

Hukumar ‘yansandan farin kaya ta DSS na binciken Hadiman gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf su 5 bayan korafin da tsohon Gwamnan jihar, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya shigar inda yake zarginsu da bata masa suna.

Wadanda aka kama din sune me taimakawa Gwamna Abba ta bangaren kafafen sadarwa, Sanusi Bature, Dawakin Tofa, da shugaban matasa na APC, Salisu Yahya Hotoro, sai Ibrahim Adam wanda shine ke baiwa Gwamna Abba Shawara kan yada labarai sannan tsohon Hadimin Kwankwaso ne, Sai Nuhu Dambazau da Mukhtar S. Yahuza.

Rahoton yace dukansu da kansu suka kai kansu ofishin DSS bayan gayyatar da aka musu.

Kwankwaso ne da kansa ya sakawa takardar korafin hannu inda ya zargesu da ci masa mutunci da bata masa suna a kafafen sada zumunta.

Karanta Wannan  A lokacin Buhari ne duk Najeriya ta susuce, saboda rufa-rufa aka rika yi, abinda ya kamata a yi sai a kauda kai, amma Tinubu ya zo gyara barnar da Buhari ya tafka ne>>Inji Dauda Kahutu Rarara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *