Tuesday, March 17
Shadow

Duk Abunda ya faru a Kano, Tinubu ne sila>>Inji Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa idan yaki ya barke a Kano to shugaban kasa, Tinubu ne sila.

Atiku ya bayyana cewa dalili kuwa shine Tinubu ya aika sojoji su je Kano su nada Sarki.

Bayan da majalisar jihar Kano ta rushe duka sabbin masarautun da tsohon gwamnan jihar, Umar Ganduje ya kirkiro, an mayar da tsohon sarki, Muhammad Sanusi akan kujerar sarautar Kano inda aka tsige Aminu Ado Bayero.

Saidai Aminu Ado Bayero bisa rakiyar sojoji wadanda ake kyautata zaton Gwamnatin tarayya ce ta bashi su ya koma Kano inda ya yada zango a karamar fadar sarki dake Nasara.

Karanta Wannan  Sanata Natasha Akpoti ta kasa kawo hujjar cewa na nemeta da lalata shiyasa ta fara bani Hakuri, kumama inda zaku san sharri ne irin nasu na mata ta kulla min, bayan tace ne nemeta da lalata ta bini min je taruka da yawa har kasashen waje kuma har hotunan Selfie ta rika dauka dani>>Sanata Godswill Akpabio

Shi kuma sabon sarki, Muhammad Sanusi II yana can fada yana karbar mubaya’a daga hakimai da sauran mutanen gari.

An dai zargi me baiwa shugaban kasa shawara, Nuhu Ribadu da hannu a baiwa Sarki Aminu Ado Bayero jirgin da ya dawo dashi Kano da kuma rakiyar sojoji, amma tuni ya karyata hakan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *