Thursday, April 10
Shadow

Duk da farashin Danyen Man fetur ya fadi a kasuwanin Duniya, ‘yan kasuwar Man fetur na Najeriya sun bayyana dalilin da farashin man fetur din yaki sauka a Najeriya

Kungiyar masu tace man fetur na Najeriya, CORAN sun bayyana dalilin da yasa farashin man fetur ya ki sauka a Najeriya duk da farashin danyen man fetur ya sauka a kasuwannin Duniya.

Sakataren yada labarai na CORAN, Eche Idoko ya bayyana cewa, dillalai dake tsakanin masu saye da masu sayar da man fetur dinne ke kawo matsalar hana farashin tashin sauka a Najeriya.

Tun a makon da ya gabata ne dai muka kawo muku rahoton cewa, farashin na danyen man fetur a kasuwar Duniya ya sauka zuwa dala $65.

Saidai a Najeriya, farashin ya ki sauka, da yake ci gaba da bayani, sakataren CORAN, Eche Idoko yace, idan ba dawo da ci gaba da sayarwa masu tace man fetur danyen man fetur din aka yi da kudin Naira ba, farashin man fetur din zai ci gaba da tashi ne.

Karanta Wannan  An kama Wannan mutumin da ya baiwa masu gàrkùwà da mutane bayanai akan me gidan da yake haya suka saceshi

Yace amma matsalar itace, dillan man fetur din dake tsakanin masu saye da masu sayarwa wanda su bama su da jari a kasuwar suna zuwane kawai su samu kudinsu su tafi, basa son a rika sayarwa da masu tace man fetur din da danyen man a kudin Naira.

Yace sun fi so a ci gaba da shigo da gurbataccen tataccen man fetur din daga kasashen waje.

Yace yanzu masu matatun man fetur a Najeriya dole sun koma saidai su sayo danyen man fetur din da zasu tace daga kasashen waje duk da gashi a gida Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *