Friday, December 5
Shadow

EFCC ta tabbatar da daure Hamisu Breaker da Gfresh a gidan gyara hali saboda wulakanta Naira

Hukumar hana yiwa tattalin arziki kasa zagon kasa, EFCC ta tabbatar da hukuncin daurin watanni 5 da akawa jarumin Tiktok, Gfresh da Mawaki, Hamisu Breaker saboda wulakanta takardar Naira.

Hukumar tace duka su biyun bayan da aka karanto musu laifukansu sun amince basu yi gaddama ba.

Babbar kotun tarayya da ke jihar Kano a arewacin Najeriya ta ɗaure shahararrun mawaƙa Hamisu Breaker da G Fresh a gidan yari saboda kama su da laifin wulaƙanta takardun kuɗi na naira.

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ce ta gurfanar da su a kotun, inda ta tuhumi Hamisu Sa’id Yusuf (Breaker) da Abubakar Ibrahim (G Fresh) da yin liƙin kuɗi yayin wasu bukukuwa.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Dangote zai sayar da wani sashe na matatar mansa

Cikin rahoton daEFCC ta fitar, kotun ta kama G Fresh da laifin “liƙawa da kuma tattaka takardun kuɗi na N1,000 da suka kai N14,000” a shagon Rahama Saidu a watan Nuwamban 2024.

Kazalika, kotun ta kama Breaker da laifin “wulaƙanta takardun naira na N200 da suka kai N30,000” yayin wani biki a garin Hadeja da ke jihar Jigawa a watan Nuwamban 2024.

Mai Shari’a S.M Shuaibu ya ce laifin ya saɓa wa sashe na 21(1) na Dokar Babban Bankin Najeriya CBN ta 2007, kuma ya yanke wa kowannensu ɗaurin wata biyar a gidan yari ko kuma tarar naira 200,000.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *