
An yi babban taron masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC a babban birnin tarayya, Abuja ranar Laraba.
An yi taronne a hedikwatar Jam’iyyar dake Abuja wanda shine irinsa na farko tun bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad ya hau mulki.
An saka jami’an tsaro sosai a wajan taron kuma masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar da yawa sun halarci taron.
Manyan Mutanen da suka halarci wajan taron sun hada da Abdulaziz Yari, Atiku Bagudu, Benjamin Kalu.
Hakanan Gwamnonin jihohin Edo, Benue, Ondo, Ekiti, Kaduna, Jigawa, Nasarawa, Yobe, Niger, Lagos, Kogi, Ogun, da Imo da kuma mataimakin gwamnan jihar Ebonyi duk sun halarci taron.
Hakanan tsaffin Gwamnonin jihohin Kogi, Kebbi, Niger, Zamfara, da Plateau duk sun halarci wajan taron.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, da Mataimakinsa Kashim Shattima da Kakakin majalisar dattijai, Godswill Akpabio dana majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas sun halarci wajan taron da misalin karfe 12 na rana.
Shugaban Jam’iyyar ta APC Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne ya jagoranci zaman.
Saidai akwai manyan fuskokin Jam’iyyar APC din da ba’a gani ba a wajan taron da suka hada da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, da tsohon Ministan Sufuri,Rotimi Amaechi.