Thursday, January 30
Shadow

Fasinjoji sun tsallake rijiya da baya yayin da jirgin Max Air yayi Hadari a Kano

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[“local”],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Jirgin Max Air ya tunkuyi ƙasa wajen sauƙa a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano

Jigin saman Max Air ƙirar Boeing 737 wanda ya dauko fasinjoji daga Lagos zuwa Kano ya tunkuyi ƙasa wajen sauƙa a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano a daren Talatan nan.

Ganau sun ce dirar jirgin ke da wuya tayar gaba ta fashe, kuma ta kama da wuta. Daga nan sai jirjin ya yi taga-taga, goshinsa ya tunkuyi ƙasa.

Tuni dai ma’aikatan kwana-kwana su ka daƙile faruwar gobara a jirgin, kuma fasinjoji su ka yi maza su ka fito daga jirgin.

Rahonanni sun nuna cewa babu asarar rayuka ko rauni ga fasinjoji da ma’aikatan jirgin.

Karanta Wannan  Ana neman a binciki matar marigayi tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu kan mutuwarsa

Fasinjoji sun tsallake rijiya da baya yayin da jirgin Max Air ya sauka a Kano

Wani jirgin saman Max Air mai lamba 5N-MBD, B733 ya yi hatsari a jiya Talata a filin jirgin saman Malam Aminu Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *