Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, dawo da taken Najeriya na daya daga cikin muhimman abubuwan da yake son yi a mulkinsa.
Ya bayyana hakane a yayin ganawa da kungiyar dattawan Najeriya, ACF.
Tinubun dai ya sakawa dokar data dawo da tsohon taken Najeriya hannu wanda hakan ya jawo cece-kuce inda mutane ke cewa ba wannan ne matsalar kasar ba.
Shugaba Tinubu ya kuma jawo hankali kan samun hadin kai a Najeriya.