Monday, December 16
Shadow

Gishiri na maganin sanyi

Eh a gargajiyance ana amfani da gishiri wajan magance cutar sanyi musamman ga mata.

Idan mace na fama da kaikayin gaba, ana samun ruwan dumi a zuba gishiri a ciki kadan a zauna a ciki na ‘yan mintuna.

Hakanan ana wanke gaban macen idan ba’a samu damar zama a ciki ba. Amma kada a tura gishirin a cikin gaban.

Za’a iya yin haka kullun sau daya har a samu sauki.

Hakanan idan ana fama da kaikayin makogoro ko hanci ya toshe, shima ana amfani da ruwan dumi a zuba gishiri a ciki a rika wasa dashi a cikin makogoron.

Karanta Wannan  Amfanin tumfafiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *