Sunday, December 28
Shadow

Gwamna Abba Kabir Yusuf zai koma jam’iyyar APC ba tare da Kwankwaso ba

Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf na shirin komawa jam’iyyar APC.

Hakan ya fito ne daga jaridar Daily Nigerian.

Jaridar tace ana tsammanin Abba zai koma APC ne a makon farko na shekarar 2026.

Hakanan jaridar tace an yiwa Kwankwaso tayin komawa APC din amma yace ba zai koma ba.

Jaridar tace akwai shirin tsige mataimakin gwamnan jihar ta Kano inda za’a baiwa Sulen Garo mataimakin Gwamnan.

A wani ci gaba da aka samu game da lamarin, Du ‘yan jam’iyyar NNPP musamman masu aiki a gidan Gwamnatin jihar ta Kano sun sanar da cewa sun amince Kwankwaso da Abba su jasu zuwa APC.

Karanta Wannan  Yanda na yi turin baro a kasar Ingila duk da cewa ni likita ne a Najeriya>>Inji Dr. Kelvin Alaneme 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *