Gwamna Dikko Raɗɗa zai fara biyan Limaman Coci alawus-alawus, zai ɗauki Malaman da za su karantar da addinin kiristanci a Katsina.

Gwamnatin Jihar Katsina ta amince da bayar da alawus-alawus ga Limaman Coci a matsayin wani ƙoƙari na haɗin kai a addinai da kuma bayar da gudummawa ga Malaman addinai.
Ƙungiyar Kiristoci ta kasa reshen jihar Katsina ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa da sakataren Kungiyar Dakta Musa Daniel Danladi ya fitar a madadin Shugaban Ƙungiyar Very Rev. Fr. Richard Shuaibu Liti.
Haka zalika, yace Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ya amince da ɗaukar Malaman da suka karanci addinin kiristanci domin karantarwa a makarantun gwamnati, inda Kungiyar CAN ta bayyana cewa hakan zai tabbatar da daidaito da ci gaba, tana mai cewa ƙungiyar ta daɗe tana neman haka.
Usman Salisu, Daga kafar Katsina Daily News
Na goyi bayan wannan tsari