Saturday, December 21
Shadow

Gwamnan Zamfara ya ɗauki nauyin karatun zaƙaƙuran ɗaliban jihar

Gwamnan jihar Zamfara a arewacin Najeriya ya ba wa wasu zaƙaƙuran dalibai 30 tallafin karatu domin su yi karatu a sakandiren gwamnatin tarayya ta Federal Government Academy da ke Suleja ta jihar Neja.

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana hakan ne a yau Alhamis lokacin da yake ganawa da ɗaliban da kuma jagorancin Cibiyar Muhammad Kabir Danbaba Centre for Women and Youth Development Center a fadar gwamnatin jihar da ke Gusau.

Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya ce cibiyar tana taka muhimmiyar rawa wajen nasarar da jihar ta Zamfara ke samu a ɓangaren ilimi. Sanarwar ta ƙara da cewa yawancin ɗaliban da suka fi samun nasara na makarantun gwamnati ne.

Karanta Wannan  'Yan Bindiga sun kashe 'yansanda 5 da sojoji 2 a Jihar Zamfara

“Wannan nasarar da kuka samu ta nuna cewa gwamnatinmu na ƙoƙari wajen inganta ilimi,” a cewar Gwamna Dauda Lawal.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *