Saturday, December 13
Shadow

Gwamnati na da arzikin da za ta ɗauki nauyin tafiye-tafiyen Tinubu ko mai yawan su – Minista

Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya ce Najeriya na da arzikin da za ta iya daukar nauyin tafiye-tafiyen da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yawan yi zuwa kasashen waje tun bayan hawansa mulki.

Tafiye-tafiyen da Tinubu ke yi zuwa kasashen waje na shan suka daga al’ummar ƙasar duba da matsalar tattalin arziki da ake fama da ita.

Sai dai da ya ke magana a shirin ‘Politics Today’ na Channels TV, Tuggar ya ce Tinubu, sabanin korafe-korafen da ake yi, har ma yana bukatar kara tafiye-tafiyen saboda mahimmancin dabarunsa da kuma amfanin da su ke da shi ga kasar.

Ministan ya bayyana cewa, Tinubu zai iya karfafa alaka da sauran shugabannin kasashen duniya ne kawai a yunkurinsa na dora kasar nan kan turba mai kyau ta hanyar yin tattaki zuwa ƙasashen..

Karanta Wannan  Hisbah ta fara kwashe yaran da ke gararamba kan titunan Kano

Ya ce, “Wannan korafe-korafen ba su da tushe. Gwamnatin nan har yanzu sabuwa ce saboda an rantsar da shugaban kasa a shekarar 2023. Ta fuskar diflomasiya, har yanzu shi ne sabon shugaban kasa. Yana buƙatar yin hulɗa da abokan aikinsa da shugabannin ƙasashe don samun damar kulla dangantaka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *