Friday, December 5
Shadow

Gwamnatin Jihar Kano ta saka dokar hana zirga-zirga na tsawon awanni 24

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ne ya ayyana dokar a taron manema labarai da ke gudana a gidan gwamnati a halin yanzu.

Ya ce an saka dokar ne domin a dakile sace-sace da fashe-fashen kayan gwamnati da na al’umma da wasu ɓatagari ke yi a ƙarƙashin zanga-zanga.

Ya ce wasu ƴan siyasa ne da ba sa don ci gaban Kano ke daukar nauyin yan daba wadanda su ka dake da zanga-zanga su ka fara kai hare-hare.

Ya kuma umarci jami’an tsaro da su gaggauta fara aiwatar da dokar nan take.

Karanta Wannan  Kungiyar Direbobin Tanka ta koka da shirin Dangote na fara jigilar man fetur dinsa inda tace zai sa su rasa aiki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *