Thursday, May 29
Shadow

GWAMNATIN JIHAR KEBBI TA AURARDA ‘YA’YA MATA 300 (DA MAZAJENSU) KARO NA 2 !

A jiya Alhamis ne (27/02/2025) Gwamnatin Jihar Kebbi karkashin jagorancin zababben Gwamnan Jihar (Comr. Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu) ta sake daurawa mata 300 aure da mazajensu , tareda duk abinda ya dace ayi musu na karramawa (auren gata kenan).

Wannan kudurin (na shirin auren gata) mai girma Gwamnan Jihar Kebbi ya sanya shi a ransa , cewa da ikon Allah zai yi iya na shi kokari don ganin gwamnatinsa ta ci gaba da bada irin wannan gudummuwa musamman ga marasa karfi , don taimakawa al’umma wajen rage yawan gwagware da kuma rage yaduwar alfasha a cikin al’umma.

Ko shakka babu wannan ba karamin alkhairi bane a cikin al’umma musamman idan sun gano hadarin da ke cikin yawaitar mabukata aure mata/maza kuma ba suda halin yin auren , a irin wannan lokacin komai na iya faruwa a kowane bangaren. !

Karanta Wannan  Majalisar Wakilai ta umarci a bada tsaro na tsawon shekaru 10 ga ɗan jaridar da ya bankado badakalar digiri dan kwatano

Muna addu’a Ubangiji Allah ya sakawa mai girma Gwamnan Jihar Kebbi da mafificin alkhairi ya kara taimakonsa a cikin wannan Gwamnatin tasa , ya iya masa da iyawarsa , kar ya barshi da iyawarsa, ya Allah kar ka ba azzalumai nasara akansa.

Wa’yannan aurarraki da aka daura muna addu’a Ubangiji Allah ya sanya alkhairai masu yawa a cikinsa , kuma ya sa Gwamnatin Jihar Kebbi tayi alfahari da shi.

Sani Musa Saminaka,
Mataimaki na musamman ga mai girma Gwamnan Jihar Kebbi (ta hanyoyin sadarwa na zamani).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *