
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta kashe Naira Biliyan 38.2 wajan kula da tsaffin shuwagabannin Najeriya a cikin shekaru 22 da suka gabata.
A wannan shakerar kawai, Gwamnatin ta ware Naira Biliyan 2.3 dan kula da tsaffin shuwagabannin Najeriya.
Ana dai kula da bukatun Shuwagabannin Najeriya irin su motocin hawa, kiwon Lafiyarsu, masu musu Hidima, da sauransu duk shekara.