Thursday, June 5
Shadow

Gwamnatin Tarayya ta sha Alwashin kammala aikin gina titin jirgin kasa daga Kano zuwa Maradi nan da shekarar 2026

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana aniyar gwamnatinsa na kammala gina titin jirgin kasa daga Kano, zuwa Jigawa zuwa Katsina zuwa Maradi.

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne ya bayyana haka a yayin da ya kaddamar da wasu ayyuka a jihar ta Katsina da gwamnatin Jihar ta aiwatar.

Shugaban kasar yace idan aka kammala wannan aiki zai taimaka wajan saukaka tafiyar mutane da safarar kaya wanda yace hakan zai rage amfani da Titi.

Hakanan shugaban kasar yace sun bayar da aikin gyaran titunan da suka hada Marabar Kankara -Dutsinma -Katsina da kuma wadanda suka hada garuruwan Zaria -Hunkuyi -Dabai da kuma wadanda suka hada garuruwan.

Karanta Wannan  Wallahi Daga Yau Na Koma Dan Izala Ganin Yadda Wasu 'Yàñ Daŕìķà Kè Mùŕña Da Rasuwàr Śhèik Iďŕis Duťsèn Tanshi Saboda Bambancin Akìda Duk Da Cewa Malami Ne Na Mùsùlùncì, Inji Abubakar Aliyu

Hakanan shugaban kasar yace suna aiki akan titin Kano zuwa Katsina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *