Thursday, February 26
Shadow

Gwamnatin Tarayya zata fara hako danyen Man Fetur a jihar Ogun

Sanata me wakiltar mazabar ogun West ya bayyana cewa jihar Ogun na daf da shiga sahun jihohin da ake hako danyen Man fetur a Najeriya.

Yace shiri yayi nisa wajan fara hako man fetur a tsibirin Tongeji dake karamar hukumar Ipokia a jihar.

Yayi bayanin ne a Ota wajan wani taro inda yace wajen na tsakanin Najeriya ne da kasar Benin Republic.

Yace an samu wannan dama ne saboda kokarin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na karfafa tattalin arzikin Najeriya.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Kalli yanda da Safiyar Yau, Laraba, Atiku Abubakar da El-Rufai sun sake komawa Kabarin Buhari suka mai addu'a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *