Monday, December 16
Shadow

Gwamnatin Tarayya zata sakawa masu samun kudi da yawa sabon Haraji

Gwamnatin tarayya zata sakawa masu samun kudi fiye da Naira Miliyan 100 sabon haraji na kaso 25 cikin 100.

Shugaban kwamitin shugaban kasa dake kula da haraji da tsare-tsaren kudade, Taiwo Oyedele ne ya bayyana haka inda yace gwamnati zata fara sakawa maau kudi sosai haraji me yawa.

Yace sabon harajin zai fara aiki ne nana da shekarar 2025.

Yace mafi yawancin ‘yan Najeriya basa biyan haraji saboda rashin yadda da gwamnati.

Yace yanzu haka kudirin dokar karin harajin yana gaban majalisar tarayya.

Yace zasu samar da yanayin da za’a rika samun bayanai kan biyan Harajin a bayyane kamar yanda kasar Afrika ta kudu ta yi.

Karanta Wannan  Matashiya Joy Amarachi Ihezie, Mai Tuka Keke Napep A Jihar Delta, Tana Da Digirinta Kuma Ta Fara Tukin Kurkura A Shekaru Uku Da Suka Gabata

Ya kuma koka da cewa kaso 17 cikin 100 na ‘yan Najeriya ne kadai ke biyan haraji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *