Wednesday, May 7
Shadow

Gwamnatin Tinubu zara dawo da shirin ciyar da dalibai na tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da cewa za ta sake ɗaddamar da shirin ciyar da ɗalibai a makarantu, ranar 29 ga watan Mayu.

Ƙaramin Ministan ma’aikatar jin-ƙai da rage talauci, Dr Yusuf Sununu ne ya bayyana hakan a ranar Larabar da ta gabata yayin wata ganawa da ƙungiyoyi masu zaman kansu da kuma jami’an gwamnati a Abuja.

Sununu ya sanar da cewa za a sake kaddamar da shirin ne domin murnar cikar shugaba Bola Tinubu shekara ta biyu akan karagar mulki.

Ya ce shirin na da nufin magance yunwa da kuma inganta ɓangaren ilimi a faɗin ƙasar baki ɗaya.

”Shirin na nufin amfanar yara miliyan 10 kuma zai iya ƙara yawan yaran da ke shiga makarantu da kashi 20 cikin 100 sannan kuma ya bunƙasa hazaƙar yara a ɓangaren karatu da kashi 15 cikin 100 ,” in ji shi.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Kalli yanda Matan Jihar Rivers suka tashi suka kama gabansu yayin da ake tsaka da taro matar shugaban kasa, Remi Tinubu na jawabi, sun ce basa son jin jawabinta, Ance bai kamata su kunyata matar shugaban kasar irin haka ba

Sake ƙaddamar da shirin na zuwa ne a daidai lokacin da ake hasashen cewa sama da ƴan Najeriya miliyan 30 na iya fuskantar matsananciyar yunwa, wanda hakan ke nuni da muhimmancin ɓullo da shirye-shirye makamantan wannan cikin gaggawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *