Tuesday, March 17
Shadow

Gwamnoni da yawa zasu dawo APC Saboda Tinubu na mulki na Adalci>>Inji Ganduje

Shugaban jam’iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da tabbacin cewa, Gwamnoni da yawa zasu sake komawa jam’iyyar.

Ya bayyana hakane a wajan taron karbar gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori da ya koma jam’iyyar ta APC.

Ganduje ya jinjinawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu saboda shugabanci na gari da yake samarwa a Najeriya.

Ganduje yace a yanzu suna da gwamnoni 22 kenan a jam’iyyar APC inda yace mutane su saka ido su gani akwai karin gwamnonin da zasu dawo APC nan gaba.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta yi aure, Ji bayani game da wanda ta aura, a ina aka daura

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *