Monday, December 16
Shadow

Gwamnonin kudancin Najeriya suna son a kafa ƴansandan jiha

Ƙungiyar gwamnonin kudu-maso-yammacin Najeriya sun nemi a kafa rundunonin ƴansanda mallakar jihohi.

Sai dai kuma sun yi fatali da fafutukar da wasu ke yi na kafa ƙasar Yarabawa zalla.

Wannan na cikin ajanda 11 da suka amince da su bayan taron da suka gudanar a Ikeja babban birnin jihar Legas a ranar Litinin.

Gwamnonin sun kuma taɓo batun sabon mafi ƙarancin albashi, inda suka yi nuni da cewa zai zo da tsarin tarayya na gaskiya.

Matsalar tsaro malace da daɗe tana ciwa jihohin ƙasar tuwo a kwarya, sai dai wasu na ganin kafa ƴansandan jihohin zai taimaka wajen magance matsalar.

A baya dai rundunar ƴansandan ƙasar ta yi watsi da irin wannan buƙata ta kafa ƴnsandan jiha a ƙasar.

Karanta Wannan  Bayan Awa 24 da yin Gàrkùwà da magaifiyar Rarara har yanzu ba'a gano inda take ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *