Wednesday, January 15
Shadow

Gyaran gashi da kwai

Ana amfani da kwai, Musamman Gwaiduwar kwai wajan gyaran gashi.

Gwaiduwar kwai itace me ruwan dorawa ko Yellow wadda ke cikin kwan idan an cire farin ruwan kwan.

Tana da sinadarai masu yawa dake taimakawa armashin gashi irin su biotin, folate, vitamin A, da vitamin D.

Mutane na amfani da Gwaiduwar kwai a gashi dan hana gashin zubewa, da kara masa tsawo, da hanashi bushewa da kakkaryewa.

Gwaiduwar kwai na hana gashi lalacewa,yana kare gashi daga abubuwan dake sawa ya lalace.

Hakanan Gwaiduwar kwai tana saka gashin kai ya rika saurin tofuwa.

YANDA AKE AMFANI DA GWAIDUWAR KWAI:

Ana iya amfani da Gwaiduwar kwai da man zaitun a kwaba a shafa a kai ko ina da ina ya shiga cikin gashi da kyau.

Karanta Wannan  Amfanin albasa a gashi

Sannan kuma ana iya amfani da kwan gaba dayanshi ba tare da hadawa da man zaitun din ba, a zuba kwan da farin da Gwaiduwar kwai din a juya da kyau a shafa a gashi.

A barshi yayi kamar awa daya sannan a dauraye da ruwan sanyi.

Ana kuma iya fara cin kwai musamman da safe dan samun gyaran gashi.

Amfani da Kwai wajan gyaran gashi bai da wata illa ta azo a gani dan haka masana suka bada shawarar cewa hanya ce me kyau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *