Saturday, December 13
Shadow

Hajji 2024: Saudiyya ta ƙaddamar da na’urar amsa fatawa ga maniyyata

Ƙasar Saudiyya ta ƙaddamar da na’urorin amsa fatawa ga masu ibada a masallatan harami.

Na’urorin za su riƙa amsa tambayoyin da ke da nasaba da shari’a da dokokin addinin musulunci.

Shafin X na Haramain ya ce an girke na’urori a harabobin masallatan harami domin bayar da fatawa ga maniyyata a lokacin aikin hajjin bana.

Masu buƙatar fatawa za su kusanci na’urorin domin tambayar abin da ya shige musu duhu, inda su kuma na’urorin za su sada su da wani malami da zai amsa tambayar nan take.

Na’urorin na karɓar fatawa da amsa ta cikin harsunan duniya 11, kamar yadda shafin Haramain ya bayyana

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda aka hada irin dakin Ka'aba a Najeriya dan koyawa Alhazai yanda zasu yi aikin Hajji, saidai wasu sun ce hakan Bidi'a ne saboda Annabi(SAW) bai ce a yi ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *